Ke uwa ce mai yara takwas, kina rainon ‘ya’yanki a sansanin ‘yan gudun hijira dake babban birnin tarayyar Najeriya bayan tserewa mummunan harin da kungiyar ta’addancin Boko Haram ke kaiwa.
Ta yaya zaki iya tinkarar barazanar rugujewar sansaninku, da kama danki, da kuma kwace baburan acabar da ki ka siya don samun abin rike rayuwa bayan duk kokarin ki na ganin kun samu rayuwa mai kyau na neman ya ci tura?